Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Bude Iyakokin Kasar


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

‘Yan Najeriya na bayyana ra’ayoyin mabanbanta dangane da shirin gwamnatin tarayya na sake bude iyakokin kasar na kasa wadanda ke garkame fiye da shekara daya.

Manoma, ‘yan kasuwa da kuma mazauna yankunan iyakar Najeriya da Nijar sun nuna goyon baya da akasin hakan dangane da wannan lamari.

Ministar kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmad ce ta furta maganar sake bude iyakokin Najeriya a makon nan.

Sai dai ba ta fadi takamaiman lokacin da kwamitin bayar da shawara akan bude iyakokin zai gabatar da rahotonsa ba.

Tuni dai wannan batun ya kawo mabambanta ra'ayoyi tsakanin ‘yan Najeriya inda wasu manoma na da ra'ayin kar a bude iyakokin yayin da wasu ke ganin bude su zai fi amma tare da daukar wasu matakai.

Shugaban kungiyar manoman alkama na jihar Kebbi kuma sarkin noman jihar Abdullah Maigandu Argungu na cikin masu ra'ayin kar a bude iyakokin.

Shi kuwa Alhaji Usman giwa Illela wanda manomi ne yana da ra’ayin a bude amma a yi gyara.

Ko bayan hana shigowa da abinci wasu na ganin ci gaba da rufe iyakokin ya shafi wasu mu'amaloli da ke wanzuwa tsakanin al'ummar Najeriya da makwabtan kasashe.

Bello Isa Ambarura Mazaunin iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar ya ce sauran harkokin kasuwanci su ma abubuwan dubawa ne ba wai abinci kadai ba.

Yanzu dai fiye da shekara daya kenan iyakokin Najeriya da wasu kasashe na garkame duk da kiraye- kirayen da aka yi wa gwamnati a wancan lokacin na ta daga kafa a bude su.

Yanzu kuma ta ce za ta bude su matakin da ta ce idan aka aiwatar watakila jama’a za su iya fahimtar ko rufewar ta yi tasiri ko akasin haka.

XS
SM
MD
LG