Kungiyar Kwallon 'kafa ta Afirka (CAF) ta Fitar da Sunayen 'Yan Wasa Biyar Aciki Za'a Zabi Zakaran Dan Wasa na Wannan Shekarar

CAF

Kungiyar kwallon ‘kafa ta Afirka (CAF) ta bada sunayen ‘yan wasa guda biyar da ake tsammanin baiwa daya daga cikin su lambar yabo ta zakaran ‘dan wasa na wannan shekarar.

‘Yan wasan dai da aka zaba daga cikin su akwai ‘yan wasan Super Eagles biyu Vincent Enyeama da Ahmed Musa, sai Yaya Toure wanda shine ke rike da wannan lambayar yabon, sai kuma dan wasan Ghana Asamoah Gyan dakuma Pierre-Emrick Aubameyang dan wasan Gabon.

Kungiyar kwallon ‘kafa ta Afirkan (CAF) dai ta tantance sunayen ‘yan wasan daga guda ashirin da biyar har zuwa biyar, kuma ‘dan wasan da aka zaba domin baiwa wannan lambar yabon za’a bayyana shi a bikin Glo-CAF Awards wanda za’a gabatar a Lagos takwas ga watan Janairu na shekara ta 2015.

A bangaren mata da suka kai wannan rukuni sun hada da ‘yan wasan Najeriya Asisat Oshola da Disire Oparanozie, sai kuma Annette Ngo Ndom ‘yar wasan Cameron da Portia Modise ‘yar wasan Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu, saikuma Zenatha Coleman ta Namibiya.

Your browser doesn’t support HTML5

Labarin Wasanni CAF - 0'50"