Manajan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Jose Mourinho, ya mayarda martani da kakkausar harshe ga Sergio Ramos da Vicente del Bosque dangane da raunukan da suka hana ‘yan wasan Chelsea Diego Costa da Cesc Fabregas buga ma kasar Spain.
‘Yan wasan biyu ba su shiga cikin sauran ‘yan wasan Spain lokacin da aka ba ‘yan wasa hutu su buga ma kasashensu ba, amma sun taimakawa Chelsea ta doke West Brom da ci 2-0 ran asabar. A bayan nan ne sai Ramos mai bugawa Real Madrid yace ya kamata wasu ‘yan wasan su nuna kudurin bugawa kasashensu, koda yake daga baya yace shi ba da wadannan ‘yan wasa na Chelsea yake yi ba.
Duk da haka, Mourinho yace ai Ramos ba likita ba ne, kuma likitocin Spain da na Chelsea duk sun duba ‘yan wasan biyu suka ce bas u cancanci bugawa kasarsu ba.
Yace, “Sergio Ramos gwanin dan wasa ne, amma shi ba likita ba ne, kamar yadda ni ma ba likita ba ne.”
Da ya juya kan del Bosque kuma, watau kwach na kungiyar kasar Spain,Mourinho cewa yayi, “Na yarda da likita na dari bisa dari. Idan har del Bosque bai yarda da likitansa ba, wannan kuma matsalarsa ce ba tawa ba. “