Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban NFF Ya Samu Shiga Kwamitin Tsare-Tsare Na CAF


Mutane sun taru a kofar ginin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya wanda ya kama da wuta ranar Laraba 20 Agusta, 2014.
Mutane sun taru a kofar ginin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya wanda ya kama da wuta ranar Laraba 20 Agusta, 2014.

Hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka, CAF, ta nada shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, a zaman memba na Kwamitin Tsare Tsare na Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2015.

Wannan Kwamitin, shi ne tamkar kwamitin kolin tsare tsaren wasanni na hukumar CAF.

A cikin wata takardar da shugaban hukumar CAF, Issa Hayatou, ya rattabawa hannu, an gayyaci Pinnick wajen bukin bude gasa ta 30 ta cin kofin kasashen Afirka ranar 17 ga watan Janairu a Malabo.

Sannan kuma, an damka masa alhakin kula da daya daga cikin cibiyoyi 4 da za a gudanar da wannan gasa ta makonni 3 wadda zata kunshi kasashe 16.

Za a gudanar da wannan gasa ta cin kofin kwallon kafar kasashen Afirka daga ranar 17 ga watan Janairu zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu a wasu birane guda 4 na kasar Equatorial Guinea.

XS
SM
MD
LG