WASHINGTON, DC —
Wasan Dambe yana da tarihi sosai a kasar Hausa, kuma har ya samu shiga cikin wasannin da ake takara kansu a duk lokacin da jihohin Najeriya suka hadu domin gudanar da wasannin motsa jiki na kasa baki daya.
A wannan hoto da ake gani, Bahago Yellow ne a hagu daga Jihar Borno, yake arangama da Bahago Balgore na Jihar Kaduna a lokacin wasannin motsa jiki na kasa na Najeriya na 18 da aka yi a Lagos a 2012.
An dauki wannan hoton lokacin gwabzawarsu ta ranar 29 Nuwamba, 2012.
A lokacin irin wannan Damben, kowane dan takara yana nade hannunsa guda daya, kuma zasu yi zagaye uku su na karawa. Duk wanda ya fadi kasa a lokacin wannan karawa, ko kuma aka doke shi ya fadi, to an kayar da shi ke nan, ko kuma an "kashe" shi a kalmar 'ytan Damben.