Mambobin Kungiyoyin Kwadagon Najeriya sun fara kargame ofisoshin Hukumar Kayyade Farashin Lantarki (NERC) da harabobin kamfanonin rarraba hasken lantar dake fadin kasar saboda karin kudin wuta.
Matakin ma’aikatan na zuwa ne biyo bayan umarnin hadin gwiwa da kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC suka baiwa mambobinsu a karshen mako na cewa su kargame ofisoshin domin nuna adawa da karin kudin wuta.
A cikin sanarwar hadin gwiwar, mai rikon mukamin Babban Sakataren Kungiyar NLCna kasa Chris Uyot da takwaransa na TUC Hassan Anka sun ce, “muna shaida muku game da shirin garkame ofisoshin Hukumar NERC dana ilahirin kamfanonin rarraba hasken na jihohin kasar nan da Abuja.
“Al’amarin wanda zai faru a lokaci guda a ranar 13 ga watan mayun da muke ciki zai kasance na hadin gwiwa. don haka, muna umartar kungiyoyin 2 suyi aiki tare akan wannan muhimmin mataki. A yayin da muke sa ran samun hadin kanku kamar kullum, muna baku tabbacin fatan alheri da jinjina.”
Manyan mambobin kungiyoyin kwadago da suka hallara a shelkwatar Hukumar Kayyade Farashin Lantarkin Najeriya (NERC) dake Abuja da safiyar yau sun hada da Shugaban Kungiyar Kwadago na NLC, Joe Ajaero, inda ma’aikatan suka bukaci a janye karin kudin lantarki nan take.
Da misalin karfe bakwai na safiyar yau Litinin, mambobin kungiyoyin kwadagon suka datse babbar kofar shiga kamfanin rarraba hasken lantarki dake garin Kaduna cikin tsauraran matakan tsaro.
‘Yan kwadagon dake bukatar a janye karin kudin wutar sun hana ma’aikata shiga harabar kamfanin rarraba hasken lantarkin.
A jihar Kwara ma, ‘yan kwadagon sun datse mashigar kamfanin rarraba hasken lantarki na ibadan dake babban birnin jihar, Ilori.
karkashin jagorancin shugaban nlc na jihar, ‘yan kwadagon sun rufe kofar shiga kamfanin tare da hana ma’aikata shiga ofisoshinsu tun daga karfe 8 na safiyar Litin din nan.
Shugaban kungiyar ta NLC, Saheed Olayinka, yace karin kudin wutar yayi mummunan tasiri akan al’ummar Najeriya don haka ya bukaci gwamnatin tarayya ta janye shi.
Ya kara da cewar, zasu ci gaba da garkame ofisoshin har sai bukatarsu ta janye kudin wutar ta cika.
‘Yan kwadagon, dauke da kwalaye masu mabambantan sakonni dake rera wakokin gwagwarmaya, sun mamaye harabar kamfanin rarraba hasken lantarkin a yayin da ma’aikatansa suka koma gefe suna jiran umarni.
Haka al’amarin yake a Akure, babban birnin jihar Ondo, inda wasu mambobin kungiyar kwadago ta TUC suka rufe shelkwatar kamfanin rarraba hasken lantarki na Benin. Inda suka taru a kofar shiga kamfanin suna zanga-zangar adawa da karin kudin wutar.
Har ila yau, a jihar Edo, shugabannin da mambobin kungiyar kwadago ta NLC sun kargame shelkwatar kamfanin rarraba hasken lantarki na BEDC dake kan titin Akpakpava na birnin Benin fadar gwamnatin jihar.
Kungiyoyi ciki harda na ma’aikatan lantarki ma na kokawa game da hatsarin da karin kudin wutar ya jefasu a ciki.
Haka ma al’amarin ya kasance a Zamfara inda mambobin kungiyoyin kwadago suka garkame ofisoshin kamfanin rarraba hasken lantarki na Kaduna dana Hukumar Kayyade Farashin Lantarki a Najeriya (NERC), tare da hana ma’aikatansu kaiwa ga ofisoshinsu.
Shugaban kungiyar TUC reshen jihar Zamfara, Kwamred Saidu Mudi, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta mayar da farashin lantarkin kamar yadda yake a baya.