Hukumomi Chadi sun tura dakaru sassan kasar don su kwantar da tarzomar da ta barke bayan zaben shugaban kasar da aka yi, inda alkaluma ke nuna cewa adadin mutanen da suka mutu a ranar Asabar ya kai 12 a lokacin hada wannan rahoto.
Akalla mutum 90 aka samu tabbacin sun ji raunuka iri-iri a N’djamena, babban birnin kasar.
Gidan talbijin na Chadi ya ba da rahoton cewa an haramta ajiye makamai ko yin amfani da su a kasar wacce ke tsakiyar nahiyar Afirka.
Rahoton ya ce an haramta makaman ne bayan da aka samu asarar rayuka tara a daren Alhamis bayan da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Mayu.
‘Yan sandan Chadi sun ce wasu mutane uku da suka ji rauni sun mutu a asibiti a N’djamena a daren Juma’a yayin da wasu fararen hula 30 suka ji rauni a wani fada da ya barke.
Shugaban mulki soja, Mahamat Deby ne ya lashe zaben shugaban kasar sai dai abokin hamayyarsa Succes Masra na kalubalantar sakamakon.
Dandalin Mu Tattauna