Wasu mazauna garin Zangon Kataf da ke kudancin Kaduna sun ce harin da 'yan bindiga suka kai a daren ranar Lahadi harin ramuwar gayya ne, sakamakon harbin wani bafillatani da ake zargin wani jami'in tsaro ya yi biyo bayan wata takaddama da ta barke a tsakaninsu.
Wani mazaunin garin Zango wanda ya nemi a sakaya sunan shi saboda dalilan tsaro, ya ce a yanzu dai an sanya dokar hana zirga-zirga.
Ya kuma ce dama akwai damuwa game da labarin kashe wani bafillatani da ya je kiwo bai dawo ba sai dai aka ga gawar shi daga baya amma jami'an tsaro su ka sha alwashin bincike kan batun, kwatsam kuma sai wannan takaddamar ta barke tsakanin wani bafillatanin da dan sanda, lamarin da ya kai ga harbi.
Kungiyar Kiristoci wato CAN ta ce harin ya tada mata hankali saboda ta yi tunanin an magance matsalar hare-haren 'yan bindiga, kamar yadda shugaban kungiyar Rabaran Joseph John Hayaf ya bayyana.
Rabaran Hayaf, ya ce har yanzu ba a san adadin mutanen da aka kashe ba, amma dai wasu na cewa mutane 10 wasu kuma na cewa 18, bayan haka an kuma yi kone-kone. Ya kara da yin kira kan gwamnati ta dauki matakan gaggawa.
Masani kan harkokin tsaro, Manjo Yahaya Shinko, ya ce akwai abubuwan da ka iya daukar hankalin al'umma game da wannan harin na ramuwa, saboda al'amari ne mai sarkakiya matuka kuma zai yi wuya a fidda batun siyasa a ciki saboda yadda ake kusantar zaben gwamnoni.
Manjo Shinko ya kuma ce sanya dokar ta baci ka iya kawo fargaba musamman a lokacin zabe.
Har zuwa lokacin wannan rahoton dai gwamnati ba ta fitar da adadin mutanen da aka kashe ba a hukumace.
Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce ta dukafa wajen kamo wadanda ake zargi don magance matsalar baki daya.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5