A wasikar da ta aikawa ministocin shara’a da na tsaron kasa, kungiyar ta bukaci sabuwar gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum ta dauki matakin samar da haske a game da kisan wasu fararen hula kimanin 317sanadin hare-haren da aka kai a watannin da suka gabata.
Harae-haren sun faru ne a gundumar Tilia dake jihar Tahoua da garuruwan Zaroumdareye da Tchambangou da Banibangou a jihar Tilabery.
Human Rigths Watch a wannan wasika ta ce idan aka dubi yanayin da abubuwa suka wakana za ta yiwu dukkan bangarorin dake kafsa wannan yaki na da hannu wajen kashe-kashen da aka fuskanta daga watan Janairu da ya gabata kawo yau a wadanan yankuna.
Idan hakan ta tabbata, ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakin hukunta jami’an da aka samu da laifi in ji ta.
Sai dai wani dan rajin kare hakkin dan adam Son Allah Dambaji na cewa irin wannan tunani abu ne da ka iya katsewa jami’an tsaro hanzarin aiki.
Shi ma shugaban kungiyar kare muradun al’umomin jihar Tilabery Amadou Harouna Maiga, na daukar bukatar ta Human Rigths Watch tamkar wani yunkurin maida hannun agogo baya a yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi Nijar da makwabtanta.
Kawo yanzu hukumomin wannan kasa ba su maida martani ba ga bukatun na kungiyar HRW ko da yake, ‘yan magana na cewa shiru ma magana ce.
A shekarar da ta gabata wani rahoton binciken hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Nijar wato CNDH ya bankado abin da ta kira kisan gillar da jami’an tsaro suka yi wa fararen hula 71 a yankin Inates ba tare da aikata laifin komai ba.
Sai dai mahukunta sun yi watsi da wannan zargi kasancewar abin na iya katsewa dakarun gwamnatin hanzari a wannan lokaci na neman bakin zaren matsalar tsaro a yankin Sahel.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5