Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama Ta HRW Ta Ce Harin Da Sojojin Burkina Faso Suka Kai Ya Kashe Fararen Hula Da Dama

Sojojin Burkina Faso

HRW ta ce ta yi hira da shaidu da dama tsakanin watan Satumba zuwa Nuwamba tare da tantance hotuna, bidiyo da hotunan tauraron bil adama.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch a yau ta zargi sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula akalla 60 a hare-haren da aka kai da jirage marasa matuka wadanda gwamnatin kasar ta ce sun harba ne kan mayakan jihadi.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce an kashe mutanen ne a wasu hare-hare uku da aka kai tun watan Agusta, biyunsu a kasuwanni masu cunkoson jama'a da kuma wani a wajen wata jana'iza.

HRW ta ce ta yi hira da shaidu da dama tsakanin watan Satumba zuwa Nuwamba tare da tantance hotuna, bidiyo da hotunan tauraron bil adama.

Kungiyar ta ce harin da jirgin mara matuki ya yi ya saba wa dokokin yaki da hare-haren da ba sa bambanta tsakanin fararen hula da harin da sojoji ke kai wa, kuma da alama wannan na cikin laifukan yaki.

HRW ta bukaci gwamnati da ta "bincika wadannan laifuffukan yaki cikin gaggawa ba tare da nuna son kai ba, tare da hukunta wadanda ke da hannu a lamarin, kuma da bayar da isasshen tallafi ga wadanda abin ya shafa da iyalansu."

A halin yanzu shugaban sojin kasar, Kyaftin Ibrahim Traore, ya mayar da hankali kan daukar tsauraran matakan tsaro kan hare-haren kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS.

Zuwa yanzu dai, gwamnati ba ta mayar da martani ga rahoton na HRW ba.