Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Fararen Hula 49, Sojoji 15 A Mali - Hukumomin Soji


Akalla farar hula 49 da sojoji 15 ne suka mutu a lokacin da masu ikirarin jihadi suka kai hari a wani sansanin soji da wani jirgin ruwa a arewa maso gabashin Mali a ranar Alhamis, in ji gwamnatin wucin gadi.

WASHINGTON, D. C - Wasu da dama kuma sun jikkata, a cewar sanarwar wacce aka karanta a kafar talbijin inda bayanai suka nuna cewa wannan adadi na wucin gadi ne.

'Yan ta da kayar bayan sun kai hari kan wani jirgin ruwa dauke da fararen hula da ke kan filayen da ambaliyar ruwa ta raba tsakanin garuruwan Gao da Mopti a lokacin damina.

Jirgin ruwan yana tafiya ne daga Gao lokacin da aka kai harin.

Maharan sun kuma kai hari a wani sansanin soji da ke yankin Bourem Circle da ke arewa maso gabashin Mali.

Kimanin maharan 50 ne aka kashe a matsayin mayar da martani, an kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku, in ji gwamnatin wucin gadi.

Kasar Mali dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da ke fama da tashe-tashen hankula masu alaka da kungiyar Al Qaeda da IS da suka samu tushen zama a Arewacin kasar tun shekarar 2012.

Mayakan sun samu galaba, sun kuma bazu a yankin Sahel da kuma kasashen yammacin Afirka da ke gabar teku, duk da dumbin kudade da kasashen duniya ke bayarwa na tallafa wa sojojin kasar.

Dubban mutane ne aka kashe tare da raba sama da miliyan shida da muhallansu a fadin yankin Sahel da ke kudu da hamadar Sahara.

Takaici game da karuwar rashin tsaro ya haifar da juyin mulkin sojoji a Mali da Burkina Faso tun daga shekarar 2020 - hudu daga cikin juyin mulki takwas da aka yi a Yamma da Tsakiyar Afirka cikin shekaru uku da suka gabata.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG