Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai Wasu Majami'u Biyu a Masar

Jami'an tsaro na musamman a Masar

Kungiyar ISIS ta yi ikirarin ita ta kai hare-hare a wasu majami'u biyu na Kubdawan Masar, da su ka yi sanadin mutuwar mutane 44 da kuma raunata sama da 100 yayin da ake ibadojin Ista.

Fashewa ta farko ta faru ne a birnin Tanta na arewacin kasar, inda babbar fashewar ta rutsa da masu ibada a Majami'ar Ts. Georges Church, inda mutane 27 su ka mutu wasu kuma 78 su ka samu raunuka, a cewar gidan talabijin din gwamnati. Kafar labaran ta ce an dana bom din ne a karkashin wata kujerar da ke babbar farfajiyar addu'a.

Jim kadan bayan nan, sai kuma aka kashe mutane 17 wasu kuma 41 su ka samu raunuka a wani harin na kunar bakin wake a Majami'ar Kubdawa da ke Iskandariya.

A Iskandariyya, Paparoma Tawados II, Shugaban Darikar ta Kubdawa, na gudanar da ayyukan ibada a Majami'ar ta Kubdawa da aka auna, to amma abin bai rutsa da shi ba, a cewar kafar labaran gwamnati.

Bayan hare-haren na bom, sai Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sissi ya kafa dokar ta baci na tsawon wata uku. "Za a dau jerin matakai, musamman ma shelar kafa dokar ta baci na tsawon watanni uku bayan an dau matakan da kundin tsarin mulki da doka su ka tanada," a cewar al-Sissi a wani jawabinsa da aka yada ta gidan talabijin.