Sai dai gamayyar kungiyoyin fararen hula a wata sanarwa da suka fitar, sun nuna cewa babu kamshin gaskiya a wannan lamarin kamar yadda daya daga cikin shugaban kungiyoyin ya bayyana.
A makon jiya ma, hukumomin kasar Nijer, sun kulle wani dan jarida mai zaman kansa Baba Alfa, dan asalin kasar Mali, saboda zarginsa da mallakar takardar zama dan kasar Nijer, ta bogi, sai dai lamarin da wasu ke ganin matakine da gwamnatin kasar ta dauka na rufe bakin dan jaridar.
Gamayyar kungiyoyin fafutukar sun bukaci hukumomi su gaggauta sakin wadannan mutane ba tare da bata lokaci ba, sa’annan sun kara jaddada aniyar cigaba da gwagwarmaya har sai masu mulki sun dawo kan hanyar gaskiya.
Kakain gwamnatin kasar Malam Issa, ya ce bazai ce kala akan wadannan korafe-korafe ba, domin a cewarsa, gwamnatinsa bata wani furuci a kan maganar dake gaban alkali.
Daga Niamay, Sule Mumuni Barma ya aiko mana da wannan rahoton.
Facebook Forum