A yau lahadi ne bama bamai suka fashe a wuraren ibadar Kiristoci har guda biyu a kasar Misra, kusan mutane 32 ne suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata, a yayinda Kiristoci yan darikar Coptic ke gudanar da bikin Palm Sunday.
Kungiyar Tsageru ta ISI ita ta dauki alhakin wannan harin.
Bom na farko ya fashe ne a Yankin Nile Delta, Arewa da birnin Cairo. Kimanin mutane 21 ne suka mutu.
‘Yan awanni kuma wani ya kara fashewa a wata cocin dake Alexandria wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11.
Shugaban kiristoci na duniya mabiya darikar Catholica ya shirya ziyartar Cairo a wannan watan domin nuna jaddada goyon bayan sa ga Al’ummar Egypt mabiya addinin Kiristanci.
Kiristoci dai yawan su ya kai kaso 10 cikin 100 na yawan al’ummar kasar Egypt. Kuma sunyi ta fuskantar barazana daga Masu tsastsauran ra’ayin addinin Islama.
Facebook Forum