A jamhuriyar Nijar yau ake cika shekaru 18 da aka yiwa tsohon shugaban kasar Nijar Ibrahim Ba’are Mainasara kisan gilla sai dai har yanzu makusantan marigayi na korafi a game da rashin sanin zahirin mutanen da suka hallaka shi duk kuwa da cewa kotun ECOWAS ta umurci kasar Nijar ta sharewa iyalinsa hawaye.
Kamar kowace shekara a bana ma magoya bayan jam’iyyar tsohon shugaban kasar Nijar Ibrahim Ba’are Mainasara, sun shirya taron adduo’I a cibiyar jam’iyyar domin tunawa da marigayin.
Makusantansa irin su Alhaji Idi Nuhu, daya daga cikin shuwagabanin jam’iyyar sun nuna takaici akan dukkan gwamnatocin da suka mulki Nijar daga 1999, kawo gwamnati mai ci yanzu suke rufa rufa game da bukatar zakulo gaskiyar lamari domin hukunta wadanda suka aika wannan kisa.
Ana su bangaren iyalin Ba’are Mainasara sun gabatar da wannan batu a gaban kotun kungiyar yammacin Afirka ta Ecowas, wace a bara ta umarci kasar Nijar data biya su diyya amma har yanzu shiru in ji Miko Isa, kakakin iyalin Mainasara.
Facebook Forum