Wani hafsin sojin Amurka yace ana tuhumar cewa mayakan kungiyar IS ne suka harba rokan da ya sauka a sansanin soja dake Arewacin Iraqi wanda kuma watakila yake dauke da gubar iskar gas ta Mustard – watau Riɗi.
WASHINGTON, DC —
A zantawarshi da manema labarai a ma’aiakatar tsaron Amurka ta Pentagon jami’in da ba a bayyana sunasa ba yace babu wanda ya samu rauni a wannan harin da aka kai sansanin sojan sama na Qayyarah amma daruruwar sojojin Amurka na jibge a wurin a lokacin harin.
Jami'in yace rokan ya fado a cikin harabar da jami’an tsaron suke amma ya kira wannan hari a matsayin mara muhimmanci ga aikin soji kuma bai da wani tasiri a kan ayyuka da sojojin ke gudanarwa ta kowace hanya.
Sansanin sojojin na Yammacin Qayyarar wuri da aka kebewa sojojin Iraqi don shirya hare hare akan garin Mosul, birnin da tun shekaru biyu da suka wuce yake zaman mazaunin mayakan kungiyar IS.