A zauren Majalisar Dinkin Duniya shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa shi ne babban manufar gwamnatinsa.
Shugaban ya shaidawa takwarorinsa cewa gwamnatinsa ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen aiwatar da yakin. Saboda haka gwamnatinsa ta rage kudin da take kashewa wajen tafiyar da alamuran gwamnati.
Buhari yace matakan da ya dauka sun zo daidai da halin da Najeriya ta shiga na matsalar tabarbarewar tattalin arziki wanda ba a Najeriya kawai ya tsaya ba, tamkar ruwan dare ne gama gari.
Yace amma tunda Najeriya kasa ce mai tasowa wajibi ne a gina tushe mai kyau da za'a dora a kai duk da matsalar da ta shiga kamar sauran kasashen duniya.
Muddin ba'a yaki cin hanci da rashawa ba batun cimma muradun karni tatsuniya ce, inji Buhari.Yayi imanin yakin da Najeriya keyi da cin hanci da rashawa yana samun nasara saboda makudan kudaden da aka sace aka kai kasashen waje an samu dawo dasu.
Inji Buhari da kudaden ne ma ake samar ma 'yan kasar ababen more rayuwa yanzu.
Shugaban ya kira kasashen da basu rabtaba hannun akan shirin yaki da cin hanci da rashawa ba na Majalisar Dinkin Duniya su gaggauta yin hakan domin Najeriya zata cigaba da kiran majalisar ta karfafa yaki da cin hanci da rashawa.
Ga rahoton Ladana Ibrahim Ayawa da karin bayani.