Wasu takardu da aka gabatarwa hukumar zaben kasar, sun cewa Clinton ta samu Dala miliyan 60 a watan Agusta idan aka kwatanta da Dala miliyan 42 da Trump ya samu.
Har ila yau Clinton ta kashe kudade fiye da Trump inda ta bashi tazarar Dala miliyan 20.
Idan kuma aka hada jumullar kudaden da ta kashe tun bayan da jam’iyarta ta tsayara da ita a matsayin ‘yar takara, ya zuwa watan Agusta, Clinton ta kashe Dala miliyan 200 fiye da Trump.
Baya ga haka an kuma ga wagegen gibi tsakanin kudaden da suka samu, inda Clinton ta samu Dala Miliyan 386 yayin da shi kuma Trump ya samu Dala miliyan 170.
Tafiyar da kamfe dai Amurka na da matukar tsada, domin kowane bangaren na da bukatar ya sayi lokuta a kafofin talbaijin domin tallata manufofinsa, sannan ga batun biyan ma’aikata da ofisoshin da ake haya a duk fadin kasar ta Amurka.