Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai Libya

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da aka kai ranar Litinin a shelkwatar kamfanin mai na kasar Libya dake birnin Tripoli, bisa ga cewar kungiyar ayyukan leken asiri ta Amurka da ake kira SITE, wadda ke sa ido kan masu tsatsautsauran ra’ayi.

An kashe ma’aikatan kamfanin biyu yayinda wadansu goma kuma suka ji rauni. Maharan kuma sun mutu a harin.

Sanarwar da cibiyar watsa labaran kungiyar IS, Amaq ta fitar tace, ta kai harin ne kan cibiyar kudin gwamnatocin ‘yan mulkin kama karya na kasar Libya.

Ofishin MDD a Libya ya yi tir da harin da ya kira “harin ‘yan ta’adda masu raki”

Kasar Libya ta tsunduma cikin rudanin siyasa tunda aka hambare aka kuma kashe dadadden shugaban shugaban kasar dan mulkin kama karya Moammar Gadhafi a shekara ta dubu biyu da goma sha daya.