Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwa Ya Karya Gadar Da Ta Hada Jamhuriyar Benin da Nijer


Ambaliyan ruwa ya ruguza gada
Ambaliyan ruwa ya ruguza gada

Karyewar gadar Malanville data Benin da kasar Nijer ta haddasa cunkoson motocin dakon kayan ‘yan kasuwan Nijer

Daruruwan treloli shake da lodi na can yanzu haka jibge a mashigar garin MALANVILLE na jamhuriyar BENIN bayan da ruwa ya ruguza wata gadar dake kan hanyar wadanan kasashe, biyu lamarin da ya haddasa damuwa a wurin ‘yan kasuwa. A saboda haka suka bukaci hukumomi su tantauna da takwarorin aikinsu na NAJERIYA da BURKINA FASO don gnin an samarda wata hanyar ratse.

Kwararowar wani harshen ruwan kogin NIGER dake kewayen garin MALANVILLE na jamhuriyar BENIN ne ya haifar da datsewar hanyar zirga zirgar a makon jiya. Lamarin ya rutsa da daruruwan motocin dakon kayan da suka fito daga tashar jirgin ruwan COTONOU akan hanyarsu ta zuwa NIJER kamar yadda shugaban kungiyar ‘yan kasuwar dake shigo da kaya daga ketare ALHAJI SANI CHEKARAOU GARO ya bayyana. Ya ce kawo yanzu akwai motoci dari bakwai da suka makale sanadiyar rashin hanya. Wadanda za su gyara gadar sun ce suna bukatar akalla kwana 45 kafin su kammala aikin gyara gadar. Alhaji Garo yace akwai kayan da ka iya baci cikin kwanakin ga kuma fargabar cewa barayi na iya farmasu su sace wasu kayan.

Datsewar hanya tsakanin NIJER da BENIN wata babbar matsala ce dake barazana ga harakokin kasuwanci abinda ka iya janyo karanci da tsadar kaya a kasuwanni. A saboda haka kungiyar ‘yan kasuwar import export ta shawarci hukumomi su tuntubi takwarorin aikinsu na kasashe makwapta domin samun mafita. Sun rubutawa Frai Ministan kasar Nijer wasika, inda suka bukaci ya tuntubi kasashe makwapta irin su Nigeria su taimaka. Ta ba da soji sur aka kayan har zuwa Kamba daga nan sais u shiga Nijer.

Kasar NIJER dake kewaye da kasashe ta kowace kusurwarta na amfani ne da tashoshin jiragen ruwan kasashen dake gabar teku wadanda suka hada da tashar COTONOU da LOME da ACCRA don sauke hajojin da ‘yan kasuwarta suka yi oda daga nafiyoyi daban daban kafin daga bisani su iso gida ta hanyar motoci.

A saurari rahoton Souley Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG