Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Maida Gawar Tsohon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ghana


An maido gawar tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya Koffi Annan zuwa kasar sa ta haihuwa Ghana inda za'a bizne shi.

Za’a aje gawar ne a cibiyar taron kasa da kasa a Babban birnin Accra har zuwa ranar Alhamis a lokacin da ake sa ran binne shi.
An maido da gawar ne zuwa kasar sa ta Ghana inda shugaba Nana Addo Dankwa Akufo, ya tarbi matarsa da iyalansa a filin jirgin saman Katoka.
Wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel kuma dan asalin Afirika na farko da ya rike mukamin babban sakataren majalisar dinkin duniya ya rasu a 18 ga watan Augusta a garin Bern na kasar Switzerland yana da shekaru 80.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG