Kungiyar ‘yan ta’adda ta IS ta dauki alhakin munanan hare-haren da aka kai a Sri Lanka a ranar Easter, inda ta ayyana cewa, martani ne kan kasashen da suka hada kai, suka yi galaba akanta a kasar Syria a watan da ya gabata, wato kasar da ta ayyana a matsayin daularta.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a hukumance, ta ce, maharanta bakwai ne suka auna mujami’un da otel-otel din, inda mutane daga kasashen da suka yi galaba akanta suke ciki, kamar yadda kungiyar nan da ake kira SITE mai tattara bayanan sirri ta fassara.
Mafi akasarin mutanen da suka mutu, ‘yan kasar ta Sri Lanka ne, amma jami’ai sun ce, akalla mutum 38 ‘yan kasashen waje ne, wadanda suka fito daga Burtaniya, Australia, Turkiyya, Denmark, Holland, India, China da kuma Amurka.
A jiya Talata, Firai ministan kasar ta Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya ce, mai yiwuwa hare-haren na da alaka da kungiyar ta IS
Hare-haren na Sri Lanka, sun yi sanadi mutuwar mutum sama da 300, kana wasu 500 sun jikkata.