Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sri Lanka: Dumbin Rayuka Sun Salwanta a Hare-haren Mujami'u, Otel


Daya daga cikin Coci-cocin da aka kai hari a Sri Lanka, ranar 21 watan Afrilu 2019.
Daya daga cikin Coci-cocin da aka kai hari a Sri Lanka, ranar 21 watan Afrilu 2019.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press, ya ruwaito jami’an tsaro suna cewa, ta yi wu fashe-fashen da aka ji guda biyu, sanadiyar hare-haren kunar bakin wake ne.

Jami’ai a kasar Sri Lanka, sun ce an kai hari a wasu Coci-coci guda uku da wasu otel-otel otel uku a yau Lahadi a kusan lokaci guda.

Sama da mutum 50 ne rahotanni suka ce sun mutu, kana wasu 300 suka jikkata a hare-haren.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press, ya ruwaito jami’an tsaro suna cewa, ta yi wu fashe-fashen da aka ji guda biyu, sanadiyar hare-haren kunar bakin wake ne.

Hukumomi sun ce Cocin Saint Anthony na daya daga cikin mujami’un da aka kai harin, sannan otel-otel din uku na wajen Colombo ne, babban birnin kasar.

Sauran mujami’un sun hada da Saint Sebastian da ke Negombo da kuma wata mujami’ar da ke Batticoloa.

Babu dai wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare-hare.

Harin na faruwa ne, yayin da Kiristoci ke fara bukuwan Easter a duk fadin duniya.

Kiristocida dama, sun kwashe daren jiya Asabar, suna addu’o’i, a wani mataki na sharar fagen fara bukuwan Easter a yau Lahadi, wanda akan yi a kowacce shekara.

Bikin na tunawa da lokacin da Kiristocin suka yi amannar cewa, Yesu Almasihu, wato Annabi Isa Alaihissalatu wasalam, ya tashi bayan mutuwarsa.

A daren jiya, shugaban darikar Katolika a duniya, Paparoma Francis ya gudanar da addu’o’i a Mujami’ar Saint Peter da ke Vatican.

A sauran sassan duniya kuwa, masu ibada sun fita zuwa Coci-coci, domin yin addu’o’i na marabtar bikin na Easter, wanda akan yi ziyarce-ziyarce, liyafa da dinke-dinke kayayyakin sawa, musamman ga kanana yara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG