Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Ta-Baci a Sri Lanka


wasu jami'an tsaron kasar Sri Lanka a bakin aiki
wasu jami'an tsaron kasar Sri Lanka a bakin aiki

Yadda aka yi amfani da kwarewa wajen tsara wadannan jerin hare-hare guda takwas, wadanda aka auna su kan majami’u da otal-otal, ya girgiza kwanciyar hankalin da aka shafe shekaru wajen 10 ana mora a wannan kasa.

Kasar Sri Lanka ta kafa dokar ta baci, bayan da ta zargi wata karamar kungiya mai tsattsauran ra’ayin Islama, da kai harin nan da ya yi sanadin mutuwar mutane 290 da raunata wasu daruruwan mutane, a ranar Easter ta Lahadi.

Gwamnatin kasar ta ce ta na kan binciken ko shin wannan kungiyar na da alaka da wata kungiyar ta’addanci ta kasar waje, ko da yake, Firaminista Ranil Wickremesinghe ya tabbatar cewa, gabanin aukuwar lamarin, kasar ta samu wani bayanin sirri daga hukumar leken asirin wata kasa, mai nuna cewa ana shirin kai wannan harin.

Yadda aka yi amfani da kwarewa wajen tsara wadannan jerin hare-hare guda takwas, wadanda aka auna su kan majami’u da otal-otal, ya girgiza kwanciyar hankalin da aka shafe shekaru wajen 10 ana mora a wannan kasa ta kan tsibiri, ya kuma kada masu bincike da jami’an gwamnati.

“Ba mu yadda cewa wadannan hare-haren wata kungiya ta wasu mutanen kasar nan ne ta kai ba,” abin da mai magana da yawun gwamnatin kasar, Rajithta Senaratne ya gaya ma manema labarai kenan. Ya kara da cewa, “Duk yadda aka yi, akwai wata alaka tsakanin harin da wata babbar kungiyar kasa da kasa.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG