Bayan da aka shafe lokaci mai tsawo cikin yanayin ta ci ba ta ci ba rundunar hadin guiwar kasashen G5 SAHEL ta kaddamar da aiyukanta gadan gadan a fagen fama domin farautar ‘yan ta’addan da suka kafa sansani a arewacin Mali kuma a cewar hukumomin tsaron jamhuriyar Nijar, suka ce ba gudu ba ja da baya a game da wannan yaki.
A taron manema labaran da Ministan tsaron kasar Nijar Alhaji Kalla Mukhtar, yace yanzu haka kasashen G5, SAHEL, sun kirke askarawan su akan iyakokin Burkina Faso, Nijar da Mali, dfomin kakkabe ‘yan ta’adda a matsayin wani matakin share hanyar kai gagarumin farmaki a arewacin Mali, yankin da ake dauka a matsayin matattaran masu tayarda kayar baya.
Fiye da dala Amurka, miliyan dari hudu ne ake bukata domin tafiyar da aiyukan rudunar G5 SAHEL, amma kawo yanzu kasar Faransa, da tarayyar Turai, da kasashen Nijar, Mali Mauritania da Burkina Faso, sun bada gudunmawar dala miliyan dari da takwas.
A baya bayan nan kasar Amurka, ta bada dala miliyan sittin abinda ke nufin kasashen duniya sun fara canza tunani dagane da tasirin wannan rundunar.
Mutuwar wasu dakarun Amurka hudu da na Nijar suma hudu a sakamakon kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai masu a farkon watan jiya a kauyen Tongo Tongo, na cigaba da hadasa cacar baki sai dai Ministan tsaron kasar ta Nijar, yace ‘yan Nijar sun gane cewa Amurkawa na iya yin yaki tare da takwarorinsu ‘yan Nijar, har a mutu domin Amurkawa dauki suka kawo wa Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5