Makon jiya ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa hukumar bunkasa yankin arewa maso gabashin Najeriya, yankin da ya kwashe shekaru yana fama da rikicin Boko Haram.
An kafa hukumar ne domin ta taimakawa al’ummar yankin da alatilas alamuransu suka koma baya musamman harkokin ilmi, kiwon lafiya, tsaro da duk abubuwan da suka shafi harkokin rayuwar jama’a.
Kusan duka jihohi shida dake yankin suka yi fama da hare-haren ‘yan Boko Haram amma jiha daya da ta fi kowace jiha fama ita ce jihar Borno sai kuma mabiye da ita, Adamawa.
A jihar Borno ne ‘yan kungiyar Boko Haram suka mamaye kananan hukumomi ishirin da biyu cikin ishirin da bakwai. Sun mallaki kananan hukumomin har zuwa lokacin da gwamnatin yanzu ta zo kana sojojin Najeriya suka kwato wuraren.
Masana sun yi kiyasin cewa za’a kwashe shekaru hamsin kafin yankin, musamman jihar Borno ya koma yadda yake da.
Ta dalilin haka ne al’ummar Borno suka yi maraba da jin labarin kafa hukumar da zata taimaka wurin bunkasa yankinsu.
Muryar Amurka ta zagaya ta ji ra’ayin mutanen jihar Borno akan kafa wannan hukumar.
Ali daga Konduga ya ce fatansu shi ne Allah ya tabbatar masu cikin koshin lafiya da kuma fatan wadanda za’a sa su gudanar da hukumar zasu tsare gaskiya. Shi ma Mustapha cewa ya yi Allah ya sa mahukumta su yi aikin da zuciya daya
Malam Ibrahim na fatan idan an kawo aikin Borno za’a koyas da matasa sana’ao’in hannu. Yau ko na ganin hukumar zata sharewa mutane hawaye.
Sanata Muhammad Ali Ndume mai wakiltar kudancin Borno wanda ya fara gabatar da kudurin kafa hukumar yana korafin kudin da aka ware domin tunkarar matsalolin yankin ya yi kadan. A ganinsa kudaden sun yi kadan matuka. Naira biliyan arba’in da biyar da aka ware ba zasu kai koina ba ganin cewa ko kasashen waje sun tara fiye da Naira biliyan dari biyu. Ya bukaci a kara kudin.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum