Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Shugabar Myanmar Ta Ziyarci Jihar Rakhine Inda Rohingya Musulmai Suka Fi Yawa


Shugabar Myanmar a ganawarta da Musulmai 'yan Rohingya
Shugabar Myanmar a ganawarta da Musulmai 'yan Rohingya

A karon farko tun bayan mummunan matakin soji da aka dauka a kan Musulmi ‘yan kabilar Rohingya, jagorar kasar Myanmar, Aung Suu Kyi, ta kai ziyara jihar Rakhine mai fama da rikicin da ke faruwa a arewacin kasar.

A jiya Alhamis Suu Kyi ta hadu da al’umar Musulmi a kauyen Pandawapyin da ke kusa da Maungdaw.

Sashen Burma na Muryar Amurka, ya ruwaito cewa shugaba Suu Kyi ta fadawa mazauna kauyen cewa tana son ta ga an sake gina masu gidajensu, inda ta yi kira ga wadanda aka dorawa alhakin aikin da su maida hankali kan muhimman bukatun mazauna kauyakan idan sun tashi yin aikin.

A baya shugabanin duniya sun yi ta sukan shugabar ta Myanmar wacce ta taba lashe lambar yabo ta Nobel, kan yadda ta nuna jan kafa wajen daukan matakan dakile rikicin.

Da farko Suu Kyi, ta yi ikrarin cewa an yi ta yada dumbin bayanan da ba na Gaskiya ba, kan halin da ‘yan kabilar ta Rohingyan suka shiga sanadiyar rikicin

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG