Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa ta Fadi Dalilin Karanci Mai a Najeriya

Ministan harkokin A Najeriya

Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, tace rashin biya dillalan mai na daya daga cikin abubuwan da ya kawo karancin man fetur a Najeriya.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur na kasa Aminu Abdulkadir, ne ya furta haka a wata hira da suka yi da wakilin mu a Abuja.

Ya kara da cewa tankokin daukan mai an yi sune don daukan mai daga defo zuwa gidajen mai.

Amma yanzu sai jigila su keyi na daukan mai daga Legas zuwa sassa daban-daban na kasa, wanda haka dole ne ya kawo jinkiri.

Shugaban yace babu yanda za'a maida tankokin daukar mai su zama tamkar layin bututun mai da ake amfani dashi wajen turo mai zuwa defo-defo.


Your browser doesn’t support HTML5

Dalilin Karancin Man Fetur - 3'25"