A wata sanarwar da suka fitar a karkashin inuwar kungiyarsu ta CIRAC, tsofaffin jami’an da suka shafe shekaru da dama wajen kare martabar Nijar, sun nuna damuwa a game da yadda ayyukan ta’addanci ke kara tsananta kusan a kowacce rana.
Halin da ake ciki a yau bayan shafe shekaru da dama na yaki da kungiyoyin ta’addanci a Nijar, ya sa kungiyar CIRAC aza ayar tambaya dangane da tasirin matakan da hukumomi ke cewa suna dauka da nufin tunkarar matsalar tsaro.
Dubun dubatar sojojin kasashen waje wadanda galibinsu na yammacin duniya ne ke girke a yankin Sahel da sunan yaki da ta’addanci, amma kuma bayanan da ke fitowa daga fagen daga na nuni abin yana neman ya gagari kundila.
Kungiyar CIRAC a wannan sanarwa ta zo da wasu shawarwarin da take ganin ita kadai ce mafitar ta’asar da ‘yan bindigar arewacin Mali ke tafkawa a jihar Tilabery.
Saurari cikakken rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5