Kungiyar kwallon kafa ta Ingila Chelsea ta yi sabon koci bayan an dade ana rade radin wanda zai maye gurbin Jose Morinho wanda ya raba gari da kungiyar.
kocin kasar Italiya Antonio Conte mai shekaru 46 ne ya sami wannan aikin da zai soma a wannan bazara zai fara aikin kwantaragin sa na shekaru 3.
Wanda ya gaji Morinho a zaman wucin gadi zai ci gabab da horas da 'yan wasan kungiyar ta Chelsea ya zuwa karshen wannan kakar wasannin.
Conte wanda ya sami nasarar lashe kofin gasar wasannin Siri A a cikin dukkan shekaru uku da yayi yana shugabancin Juventus zai kasance dan kasar Italiya na biyar da zai horas da 'yan wasan na Chelsea.
\An dora ma Conte nauyin dawo da martabar kungiyar ta Chelsea wacce ta fuskanci gagarumin koma baya bayan ta lashe kofin Premier, ranar 17 ga watan disamba ne abincin Morinho ya kare a kungiyar ta Chelsea biyo bayan mummunan farawa a gasar kakanni.