Kamar yadda muka ji ra'ayoyi mabanbanta da dama daga bakin samari matasa dangane da irin abubuwa 5 da sua fi kauna ko so masoyan su su rika yi masu, yau mun sauya akalar shirin ne wajan 'yan mata domin jin tabakin su.
'yan matan sun bayyana cewar suna matukar kaunar masu kulawa da su kamar yadda masu iya magana suka ce zuciya na kaunar mai kyautata mata, dan haka kyautatawa na daya daga cikin muhimman abubuwan da suke bukata.
Kodashike wasu daga ciki sun nuna cewa idan masoyi ya nuna ya damu da masoyiyar sa, bau yadda zai bata lokaci ba tare da yaji daga gareta ba dan haka a cewar su ganawa akai akai na daya daga cikn abubuwan da suke kauna.
Masu iya magana sun ce yaba kyauta tukwici, wasu daga cikin 'yan matan sun ce lallai kyauta bata kadan, wato ko yaya take takan kara dankon zumunci inda yawancin lokuta zaka ji kana son ganin masoyin ka badan komi ba sai daomin kyautatawar nan da yake maka.
Saurari cikakkiyar hirar.