Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Yan Wasan Kwallon Kafar Najeriya Sun Samu Koci Dan Kasar Waje


Tun bayan rashin nasarar ‘yan wasan kwallon kafar Super Eagle, a gasar cin kofin duniya na kasashen nahiyar Afrika AFCON na shekarar 2017, kungiyar tasamu sabon koci dan kasar waje da zai ja ragamar kungiyar. Sabon kocin dan kasar Faransa Paul Le Guen, ana sa ran zai horas da ‘yan wasan na kungiyar.

Ana sa ran zai sa hannu a kwantiraki na shekaru biyu, wanda za’a iya sabunta kwantirakin idan yayi wata rawar gani. Koci din Mr. Paul, ya bukaci hukumar kwallon kafar Najeriya da su sama mishi gida a babban birnin tarayya Abuja, da kuma wani gida a birnin Lagos, domin zai dinga kaiwa da kawowa a tsakanin yankunan don bama ‘yan wasan duk dubarun wasa da suka kamata.

An kiyasta abun da za’a dinga ba shi a duk wata da suka kai kimanin naira milliyan goma sha biyu. An dai haifi kocin ne a shekarar 1964, yana dai da shekaru 52, kuma shi tsohon dan wasa ne, ya kuma tabayin shugaban klob din kasar Oman National Team.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG