Fitaccen dan wasan kwallon kafar duniya na kungiyar FC Barcelona, Lionel Messi, ya aika ma ‘yayan shugaban kasar Amurka, da rigar kwallo mai lamba 10, bayan ya saka hannu a jikin rigunan. Ita dai wannan kyautar ya rubuta sunan su a jikin rigar “Sasha” da “Malia”
A lokacin da suka kai wata ziyara a birnin Buenos Aires, na kasar Argentina, a satin da ya wuce, shugaban Amurka Barak Obama, ya bayyanar da cewar ‘yayan nashi sun so su hadu da dan wasan Lionel, amma hakan bai samu ba. Dan wasan Lionel Messi, ya bayyanar da wannan ziyar ta shugaban kasa da iyalanshi a matsayin wata babbar ziyara.
Ya bayyanar da cewar gaskiya da ya samu haduwa da su da kuwa yaji matukar dadin haduwa, amma tunda hakan bai samu ba, bari ya aika musu da kyautar girmamawa. Dan wasan dai ya aika da wannan sakon nashi ne ta hannun shugaban kasar shi ta Argentina, Mr. Mauricio Macri, a lokacin da yake kokarin halartar taron makamshin Nuclear da aka gudanar a kasar Amurka.