Mayakan kungiyar Boko Haram sun sanar da yin mubaya’a da kungiyar ISIS, yayin da a ke samun rahotannin tashin bama-bamai da suka hallaka sama da mutane hamsin a jihar Borno inda kungiyar Boko Haram ta ke da karfi.
Kungiyar da ke sa ido kan ayyukan ta’addanci mai suna SITE, ta ambaci ta bakin kungiyar Boko Haram jiya ta na cewa, “mu na mubaya’a da Kalifa” a wani sabon bidiyo da a ke kyautata zaton ya fito ne daga kungiyar mayakan Najeriya.
Kungiyar ISIS ta na iko da wadansu sassan Iraq da Syria kuma ta na kiran shugabanta Kahlifa.
Sanarwar ta biyo bayan wadansu hare-hare da a ka kai a Maiduguri babban birnin jihar Borno da ya yi sanadin rasuwar sama da mutane 55 kimanin 140 kuma su ka ji raunuka.
Wakilinmu Haruna Dauda Bi’u na da karin bayani dangane da hare-haren da a ka kai a jihar Borno.
Your browser doesn’t support HTML5