Kungiyar Boko Haram ta sako mata da yara dari da hamsin da takwas data sace daga kauyen Katarko na jihar Yobe, harma an mika su ga iyalansu a garin Damaturu.
Kungiyar Boko Haram ta sako wadannan mutane bayan ta tsare su har na tsawon makoni uku.
Kwamishinan adalci wanda kuma sine shugaban kwamitin sake tsugunar da wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu Ahmed Goniri shi ne ya yiwa yan jarida bayani a Damaturu a ranar Alhamis.
Daya daga cikin matan da aka sako, tace 'yan yakin sa kan basu musguna musu. Sun dai gaya musu cewa idan basu sha'awar addinsu to za'a sake su. Kuma hakan ya faru, aka sako su.
Gwamnatin jihar Yobe ta taimakawa mata wadanda suka rasa mazajensu da kuma wasu mata taimakon kudi da kayayyakin abincin.
Your browser doesn’t support HTML5