WASHINGTON, D.C —
Ganin yadda 'yan kungiyar Boko Haram suka bayyana a yankin Diffa, kasar jamahuriyar Nijer, suka tursasawa dubban mutane gudu daga gidajen su, yanzu haka hukumomin Maradi, sun fara fadakar da matasa su guji shiga kungiyar ta'addanci.
Mataimakin shugaban Majalisar dokokin yankin Maradi, Mahaman Siraji Moussa ya shaidawa wakilin Sashen Hausa Chaibou Mani cewa matasa sun yi tururuwa sun amsa kira tare da yin alkawarin cewa ba za su yarda a yi amfanin da su a yi ta'addanci ba.
Duka wannan na faruwa ne adaidai lokacin da gwamnatin kasar Nijer ta dauki tsaurara matakan tsaro a yankin Diffa inda sojoji ke artabu da 'yan Boko Haram.
Mallam Mahaman Siraji Moussa ya kara jaddada mahimmancin addu'a tare da yin kira ga jama'a da su tashi haikan su dage da rokon Allah, Ya kare Maradi daga sharrin ta'addanci, Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk kasar jamahuriyar Nijer, da ma duniya baki daya: