Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Kokarin Kwato 'Yan Matan Chibok - inji Gwamnati


Mr.Mike Omeri shugaban cibiyar bayyana manufofin gwamnatin Najeriya game da yaki da ta'addanci.
Mr.Mike Omeri shugaban cibiyar bayyana manufofin gwamnatin Najeriya game da yaki da ta'addanci.

Mike Omeri, wani mai magana da yawun gwamnatin Najeriya ya tabbatar da cewa sojojin kasar na gudanar da ayyuka a gandun dajin Sambisa, sannan gwamnati na kan bakanta na gani an ceto daliban Chibok bayan share sama da kwanaki 310 da sace su.

Shugaban cibiyar bayyana manufofin gwamnatin Najeriya musamman ma game da yaki da ta'addanci Mr. Mike Omeri ya amsa tambayoyin da Madina Dauda ta yi ma sa akan batutuwan da suka hada da kubutar da 'yan matan Chibok, da kuma kakkabe 'yan Boko Haram cikin makonni shida.

Mr.Mike Omeri ya bayyana abun da shugaban kasar Najeriya ke nufi da furucin da yayi cewa watakila za'a gano 'yan matan Chibok kafin karshen wa'adin makonni shiddan da aka diba a yi yaki da 'yan Boko Haram kuma a yi zabe.

Mr.Mike Omeri ya ce mutane sun fassara maganar yadda suka fahimta, amma abun da shugaba Goodluck Jonathan ya ce shi ne, a cikin makonnin nan shida da aka diba za'a yi kokarin kwato 'yan matan Chibok, kuma a kokarta samar da dan kamannin zaman lafiya a wurare, ba don a yi zabe kawai ba, amma don ma mutane su koma gidajen su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG