Kungiyar Alkalai A Nijer Ta Yi Allah Wadai Da Sabawa Dokar Kotu

A jamhuriyar Nijer kungiyar ''SAMAN, ta alkalan shari’a, ta nuna bacin rai akan yadda masu fada a ji a kasar ke kin mutunta hukuncin kotu, haka ya sa kungiyar ta bukaci shugaban kasa Mahamadou Issouhou, ya tsawata wa masu wannan muguwar dabi’a dake barazana ga dimokradiya.

A yayin wani taron maneman labaran da suka kira a cibiyar kungiyar su ta ''SAMAN alkalan shari’a sun yi tir da Allah wadai da abinda suka kira sabawa hukuncin kotu, inda masu shari'a ke cewa dabi’a ce dake kokarin zamewa wasu kusoshin gwamnatin Nijer jiki, a cewar Zakar Yaou Mahamadou, sakataren tsare tsaren kungiyar alkalai ta kasa.

Ku Duba Wannan Ma Wane Tasiri Janyewar Dakarun Amurka Daga Nijer Zai Yi?

A ci gaban wannan sanarwar, kungiyar alkalan ta yi kiran hukumomi su gaggauta gudanar da bincike domin zakulo masu hannu a satar da ake zargin an tafka a jarabawar jami’ar shari’a ta baya bayan nan da aka yi.

A lokacin da wakilin Muryar Amurka, ya tuntubi kakakin gwamnatin Nijer, Minista Abdourahman Zakari, dake bangaren zartarwa akan wadanan korafe korafen, ya sanar cewa yana cikin wani aiki.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Alkalan Shari'a A Nijer Sun Tir Da Allah Wadai Da Sabawa Dokar Kotu 3'01