Duk da yake kawo yanzu shuwagabanin rundunar mayakan Amurka ba su yanke wata takamaimiyar shawara ba akan batun duba hanyoyin janye dakarun wannan kasa daga nahiyar Afirka jama’a na kallon matakin ta huskoki da dama.
Alkassoum Abdulrahaman mai sharhi ne aakan alamuran tsaro na ganin janyewar dakarun Amurka daga kasashen Afirka, musamman daga Nijer da Mali da sauransu, zai kawo wani cikas musamman ga sojojin Faranshi domin zasu kasance su kadai, kuma su kadan ba za su iya aikin dake gabansu.A gaskiya abun dake fuskantar kasashen ya fi karfinsu idan aka yi la'akari da abubuwan da suka faru a Syria, Iraqi, Afghanistan da dai sauransu.
Tasana'antar aiyukan ta’ddanci a yankin Sahel ya sa kasashen yammaci mayarda jamhuriyar Nijer tamkar wata sansani lamarin dake shan suka daga jami’an fafitika irinsu Dambaji Son Allah saboda haka yake cewa abin farin ciki ne idan Amurka ta tabbatar da shirin janyewar sojojinta daga wannan kasa.
Makuddan kudade ne kasar Amurka ke kashewa domin aiyukan tsaro a kasashen dake fama da ta’addanci sabili kenan da mai sharhi akan al’amuran tsaro Dr Sani Yahaya Janjouna ke danganta shirin ficewar sojan Amura da dalilai masu nasaba da matsin tattalin arziki. A cewarsa anfanin da Amurka ke samu a kasar Nigeria ba za'a kwatantashi da na kasar Nijer ba idan har ma tana samun wani abu ke nan. Nigeria na da man fetue da wasu albarkatun da babu su a Nijer.
Ko da yake wasu na kallon ficewar sojan Amurka a matsayin wani koma baya ga sha’anin tsaro a yankin Sahel ta wani bangaren matakin zai ba sojan Nijer damar su gaji dukkan ingantattun kayan yakin da Amurka ta girke arewacin kasar.
Asaurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum