Hukumomi a Somalia sun ce akalla mutane 30 aka kashe a jiya Lahadi bayan da wasu tagwayen bama-bamai suka tashi a garin Baidoa.
WASHINGTON DC —
‘Yan sanda da hukumomin karamar hukumar garin sun ce lamarin ya faru ne a tsakiyar garin na Baidoa, wanda ke da tazarar tafiyar kilomita 245 daga Mogadishu babban birnin Somalia, kuma harin farko wanda aka dasa bam a wata mota ya auku ne yayin da ake hada-hadar kasuwanci.
Harin na biyu kuwa, wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani gidan cin abinci.
Hukumomin sun ce baya ga mutane 30 da suka mutu, akalla wasu 40 kuma sun jikkata
Wadannan hare-hare na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wasu munanan hare-hare da aka kai a kasar wadanda suka kashe mutane 25 kana wasu 65 suma suka jikkata a Mogadishu.
Kungiyar Al Shabab da ake alakantawa da ta Alqaeda ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare.