Mai magana da yawun rundunar sojan kasar Mr. David Obonyo ya fadawa manema labarai yau Alhamis cewa, an kashe Mahad Karate wanda kuma aka sani da sunan Abdirahim Mohamed Warsame, tare da wasu manyan kungiyar su 10 a wani hari ta sama da aka kai a kudancin Somaliyya ranar 8 ga watan nan Fabarairu.
Wani shafi mai goyon bayan kungiyar al-Shabab a yanar gizo yace wannan rahoton ba gaskiya ba ne, kuma Karate na nan kalau, sanarwar kuma ta ce babu wani hari ta sama da ya taba sansanin.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da bada tukuicin dala miliyan 5 ga duk wani mai bayanin da zai kai ga hukumta Karate. Ma’aikatar ta ce ya taka muhimmiyar rawa a Amnyiat, wani reshen kungiyar al-Shabab da ya kai hari a Jami’ar Garissa da ke Kenya a watan Afirilun bara, wanda ya hallaka kusan mutane 150.
Kungiyar dai ta kai hare-hare a Kenya tun bayan da gwamnatin kasar ta tura dakarunta kasar Somaliyya don yaki da ‘yan al-Shabab a shekarar 2011.