Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana alkalumman ne yayin da yake amsa tambayoyi a kafar tashar talibijan ta Somalia daren Laraba yayin da aka tambayaeshi abun da ya sa ya kasance a addu'ar tunawa da sojojin a kasar Kenya.
Shugaban yace "lokacin da aka ce sojoji 180 zuwa 200 da suke kiyaye zaman lafiya a kasarmu aka kashe, ai abun damuwa ne".
Mai magana da yawun dakarun tsaron Kenya David Obonyo ya yi saurin musanta ikirarin shugaban Somaliyan a wata jaridar Kenyan mai suna 'The Star". Yace watakila ikirarin kungiyar al-Shabab ce ta rudar da shugaban saboda yawan wadanda aka ce an kashe sun fi na kamfani guda..
To saida Kenya bata taba bayyana yawan sojopjinta da aka kashe ba a garin El Adde amma ta amince an kashe mata sojoji da dama.
Ita kungiyar Al Shabab tace ta kashe sojojin Kenya fiye da 100