Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ga Hotunan Mutumin Da Ya Haddasa Fashewar Jirgin Somaliya


Kamfanin jirgin Daallo
Kamfanin jirgin Daallo

Hukumomin kasar Somalia sun ce na’urar daukan hoton da aka dasa a filin tashin jirage, ta nuna hotonon bidiyon wasu mutane biyu suna mika wa fasinjannan da ya mutu, wata na’urar computer ta tafi da gidanka, gabanin wata fashewa da aka samu a lokacin jirgin na cikin tafiya a ranar Talatar da ta gabata.

Kakakin gwamnatin Somalia, Abdissalam Ahmed Ato, ya gayawa Muryar Amurka cewa hotonan bidyon sun nuna yadda mutanen biyu suka mikawa mutumin na’urar computer a asirce.

Haka zalika hotunan sun nuna cewa lallai mutumin ne ya rasu bayan da aka samu fashewar.

A kwanakin baya, wani jami’in tattara bayanan sirrin kasar, ya gayawa Muryar Amurka cewa, ana tsare da wasu ma’aikatan filin tashin jiragen da na kamfanin jirgin Daallo domin a tuhume su.

A cikinsu har da wasu mutane biyu da ake ganin babu haufi su suka taimaki mutumin da ake zargi da haddasa fashewar.

Abdissalam ya kara da cewa masu bincike suna rike da mutane 20 ya zuwa yanzu, kuma cikinsu akwai wasu ma’aikatan gwamnati da wasu ‘yan kasuwa da suka taimakawa mutumin da ake zargin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG