Sabon Kudurin Tsarin Harajin Tinubu Ba Zai Talauta Arewa Ba - Fadar Shugaban Kasa

Shugaba Bola Tinubu (Hoto: X/Bayo Onanuga)

Wasu mutane na ikirarin cewarkudurorin na adawa ne da arewa kuma an tsarasu ne domin talauta yankin.

Fadar shugaban Najeriya ta musanta kirarin da wasu keyi na cewar an tsara kudurorin sauyin tsarin haraji ne domin talauta yankin arewacin kasar.

Shugaba Bola Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin Najeriya da kudurorin ne makonnin da suka gabata saidai hakan ya janyo cece kuce.

Wasu mutane na ikirarin cewarkudurorin na adawa ne da arewa kuma an tsarasu ne domin talauta yankin.

Saidai, mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga yace babu kamshin gaskiya game da wadannan zarge-zarge.

“Kudurorin harajin ba zasu kara azurta jihohin Legas da Ribas ba tare talauta wasu sassa na kasar, sabanin yadda ake yadawa,” a cewar sanarwar da Onanuga ya fitar a jiya Litinin.

“Kudurorin ba zasu lalata tattalin arzikin wani sashe na kasar nan ba. A maimakon hakan, manufarsu shine inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman marasa galihu, dake rayuwa hannu baka hannu kwarya.”

A cewarsa, sabanin rade-radin da ake yi, babu wani sashe na kudurorin da aka tsara domin rushe wasu hukumomin gwamnati.

“Sabanin karerayin da ake yadawa, kudurorin basa nufin cewar ma’aikatu irinsu NASENI da TETFUND da NITDA zasu daina aiki a 2029 bayan an zartar da kudurorin zuwa doka” a cewarsa.