Yanzu haka an yiwa kudurin dokar karatu na farko a Majalisar kasa, amma daga dukkan alamu cece-kucen da ya taso kan matakin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da gwamnonin jihohin kasar, da manya masu fada a ji suka dauka a kan kudurin dokar, ya sa Sanata Mohammed Ali Ndume cewa zai iya tasiri, idan Majalisa za ta yi aiki akan dokar.
Ndume ya ce ya kamata a janye kudurin da ke bukatar a gyara fasalin haraji, domin ba abin da yan kasa suke bukata kenan a yanzu ba. Ndume ya ce idan ana so a duba wannan dokar har ta yi tasiri, to sai an wayar da kan al'umma sosai akai tukunna kafin a ba 'yan kasa dama su amince da dokar ko a samu akasin haka.
To sai dai kwararre a fanin tattalin arziki Shuaibu Idris Mikati, na cewa a ka’ida na dan adam ya kamata a rika sauya dokoki ko a yi wa hukunce-hukunce kwaskwarima, domin a samu gudanarwa cikin sauki. Mikati ya ce tun ba yau ba ake sauye-sauye kan haraji a kasar, kuma har sunan hukumar karban harajin ma an gyara mata fuska. Mikati ya ce yin irin wannan gyara zai taimaka wajen saita kasar.
Amma shugaban kungiyar CISLAC Auwal Musa Rafsanjani, ya yi bayanin cewa in har tsarin dimokradiya ake bi, kuma ana yin doka ne domin jama'a, ya kamata shugaban kasa ya janye dokar har sai an shirya.
Rafsanjani ya ce gwmnonin jihohin kasar da masu fada a ji sun nuna cewa lokaci bai yi ba da za a kawo wannan doka da ta shafi sauya fasalin haraji.
A watan Oktoba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya mika wa Majalisar Kasa wani kuduri da ya kunshi bangarori guda hudu na sake fasalin haraji da suka hada da dokar harajin Najeriya da dokar kula da harajin da dokar da za ta bada dama a kafa hukumar tattara kudaden shiga na hadin gwiwa.
Domin Karin bayani saurari rahotan Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5