Mr. Ardo yace “mun yi kira ga jama’ar dake zauna a tsuburin ‘Lake Chad’ a wannan gefe dake cikin Nijar, mun ce musu mun basu wa’adi zuwa Litinin karfe 6 na maraice su fito dukkansu, su dawo cikin garin Ruwan da suke waje da ruwa. Bamu ce musu kuje gari kaza, ko gari kaza, su zasu zabi inda zasu je.”
“Amma abu guda muka ce musu, su fito daga cikin tsuburi. To yanzu a lissafi da muka yi, tsuburi da abun ya shafa sun kai wajen 115” a cewar Mr. Ardo.
Sai dai wadannan mutane dake wannan yanki, noma da kiwo da kamun kifi ne sana’oinsu. Ko wani irin sana’a ne yanzu zasu yi? Mallam Ardo ya bada amsa.
“Na daya, zan ce bisa lissafi da muka yi, mutane da abu zai shafa, anyi lissafi mutanen da suke cikin garuruwan nan, zasu kai mutane dubu ishirin da bakwai da dari biyar (27,500), amman kafin mu ce musu su fito, da yawa daga cikinsu sun riga sun fito tun ba’a gaya musu ba. Kennan wadanda suka yi saura ne, ake gaya musu. Yanzu dai zamu taimaka musu, bamu san kamar kwana ko watanni nawa zasu zauna. Amman duk tsawon da abu ya kama, zamu taimaka musu.”
A karshe Mr. Ardo ya bayyana matakan da gwamnati take dauka a halin yanzu, domin gani wannan mataki yayi tasiri.
“Lallai mu da ministan harkokin cikin gida, da minista na tsaro, zuwan mu ya nufi abu biyu, tabbata ‘yan Nijar da sauran kasashen duniya, karanga yana hannun jami’an tsaro. Na biyu, ‘yan ta’adda an kore su daga nan. Mun je munga irin ta’adin da suka yi. Lallai sun yi barna, sun kashe mutane sun kona gari. To dangane da abunda suka yi wannan, shiyasa mahunkuntar Nijar suka ce ‘talakawa ‘yan uwanmu talakawa da suke can, su fito fili su shiga cikin jama’a su boye.”
Mayakan Boko Haram da suka addabi Najeriya sun fara kaiwa Janhuriyar Nijar hare-hare tun bayan shawarar da kasar ta yanke na taimakawa Najeriya yaki da mayakan Boko Haram.
Your browser doesn’t support HTML5