Banda gidan kwana da gwamnati zata tanadawa wakilan taron da motocin hawa kowannensu zai samu nera miliyan hudu wata a matsayin alawus.
WASHINGTON, DC —
Yayin da ana gaf da soma taron kasa an soma samun korafi irin abubuwan da gwamnati ta shiryawa wakilan taron inda kowannensu zai samu nera miliyan hudu wata a matsayin alawus
Muibi Magaji shugaban kungiya mai radun yaki da cin hanci da rashawa tun daga tushe yace makudan kudaden da gwamnati ta kebe da kuma nera miliyan hudu da zata biya kowane wakili wata, wato cikin wata hudu wakili guda nada nera miliyan goma sha biyu ita ce matsalar makomar abubuwan da duk za'a tattauna a wurin taron.
Magaji yace abun akwai takaici da banhaushi. Yace menen ma'anar biyan mutum nera miliyan hudu wata? Albashin shugaban kasa bai kai nera miliyan hudu wata ba sai a baiwa wanda aka gayyata taro ya zo ya tattauna abun da ya shafi kasa nera miliayan hudu. Magana ce da yakamata a yi kishi. Kamata yayi kada ma a sa kudi. Magana ce ta al'umma. Kamata yayi alumma su zabesu kana su tara masu kudin taimakawa. Al'umma ya kamata ta tura wakilansu ta gayawa gwamnati abubuwan dake damunsu ba wadanda zasu je su yi kwancinsu domin gwamnati ce ta zabesu A wannan taron babu abun da zai sake zani domin an dauko hanyar tabbatar da cewa babu abun da ya sake.
Abdullahi Ismail Kwalwa wani maisharhi a kan alamuran yau da kullum yace bai kamata a kira taron na kasa ba. Yanayin da aka zabi taron yanayi ne na kafa kwamiti ba taron kasa ba. Idan za'a yi taron kasa akwai tsari da ake bi. Idan mutane sun kai dari biyu za'a fitar da wakili daya. Amma wannan taron nadi aka yi kamar yadda zaka dauko abokai ka ce ka shiryasu su je su yi maka harkar biki ko wani abu. Saboda haka taron idan an yi ba zai fitar da wani abu da zai yi tasiri ba domin babu ma bukatarsa. Yadda talauci ya yiwa kasar katutu da gwamnatin tarayya ta fitar da taron gaggawa a yi taron yadda za'a rage ko kawar da talauci.
Ana iya taron kasa kan harkar tsaro. Kowace mazaba aka kira ta bayarda wakili a yi taro kan talauci ko tsaro za'a kawo abubuwa da yawa da za'a yi anfani dasu ko yanzu ko kuma nan gaba. Talauci ya kamata a mayarda hankali a kai ala tilas.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5