Taron ya sha suka a wurin jama'a musamman daga 'yan arewa sabanin yadda 'yan kudu suka rungumi taron. Sun yabawa shugaban kasa da shirin wannda suke ganin wani kokari ne na dunkule kasar wuri guda. Kawo yanzu dai babu wani sashe ko wata kungiya da ta nuna son ballewa daga kasar.
Kodayake wasu sun amince da taron amma tun lokacin da aka fitar da sunayen wakilai aka soma samun korafe-korafe. Wasu na ganin daga yadda aka zabi wakilan an nuna wariya da son kai da banbanci.
Mohammed Sale Banga dan majalisar dokoki daga jihar Borno yace taron yana da kyau idan za'a sami masalaha ga duk abun da kasar ke fama dashi. To saidai yace suna ganin "anya ko da adalci a wannan taron?" Yace ance wadanda suka fi yawa zasu samu wakilai mafi yawa to amma sai gashi wakilan arewa basu kai yawan wakilan kudu ba, sashen da mutanensa basu kai yawan na arewa ba. Wanan lamarin shi ya kawo shakka ta daya. Na biyu kuma wakilan jiharsu da aka zaba kusan 'yan jam'iyya daya ne abun da zai sa su tafi da manufa daya, wato su kare muradun jam'iyyar PDP. Wakilan da aka zaba a Borno tamkar mutane ne na shugaban kasa. Wannan lamarin ya kawo shakku game da taron.
Malam Muhammed na anguwar Bolori yace idan za'a yi adalci ma mutanen arewa to taron yana da kyau amma kuma idan an fito ta wata fuskar ba zai yiwa arewa dadi ba. Abun da ya damu arewa shi ne yadda za'a samu zaman lafiya ba taro ba. Mutane suna kwana su yini idanu a bude domin rashin tabbasa din tsaro. Yace kawo yanzu babu wani shugaba da ya zo cikinsu ya san abubuwan dake damunsu.
Ga rahoto.