Makasudin taron da suka shirya a yankin kudancin Najeriya shi ne domin zaburar da shugabannin kananan hukumomi 774 a kan yadda za'a yi adalci kan kudin hukumomin da kungiyarsu. Suna kuma son su wayar da kawunan shugabannin su tashi tsaye su kare mutunci kananan hukumomi da 'yancinsu da kuma kare ma'aikata. Suna son su yi anfani da taron kasa su samu abun da basu samu ba lokacin da majalisun tarayya suka yiwa kundun tsarin mulkin kasar garambawul.
A taron kasa suna son a tabbatar da 'yancin kananan hukumomi su koma karkashin mutanen karkara domin su ne ke da su. Lokaci ya zo da zasu tsayar da magana daya domin kare 'yancin kananan hukumomi. Hanya mafi a'ala kuma da za'a tabbatar da 'yancin kananan hukumomi shi ne a kakkabe hannun gwamnoni gada harkokinsu. Gwamnoni suna yiwa hukumomin shiga sharo ba shanu lamarin da ya sa suka lalatasu.
Ga rahoto.