Kotun Tsarin Mulkin Nijer Ta Cire Hama Ahmadou Daga Sunayen ‘Yan Takarar Shugaban kasa

A Jamhuriyyar Nijer kotun tsarin mulkin kasar ta bayyana sunayen mutanen da suka cancanci shiga zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan Disamba da ke tafe bayan gudanar da aikin tantancewa amma kuma ta yi watsi da wasu daga cikin 'yan takarar.

A zamanta na yammacin jiya Juma’a a karkashin shugabancin mai shari’a Bouba Mahaman, kotun tsarin mulkin kasar ta sanar da sunayen mutanen da suka cancanci shiga zaben ranar 27 ga watan Disamba. Daga cikin ‘yan takara 41 da suka shiga fafatawar. Kotun ta ce ‘yan takara 30 ne suka cika sharuddan da ya kamata.

Dan takarar jam’iyyar PNDS Bazoum Mohamed na daga cikin wadanda suka sami izinin shiga zaben, ya yi godiya ga Allah ya kuma ce zai tabbatar da ya ci gaba da aiki tare da jam’iyyar sa.

Alkalan Kotun tsarin Mulki a Nijer

Kotun ta yi watsi da takardun ‘yan takara 11 saboda rashin cika ka’ida, akasarinsu wadanda suka gaza biyan kudaden jingar da aka kayyade ne, sai kuma jagoran ‘yan adawa Hama Amadou na jam’iyyar Moden Lumana wanda hukuncin da aka yanke masa a shari’ar nan ta badakalar jarirai ta goga wa takardunsa bakin fenti.

Hama Amadou

Ya zuwa yanzu dai ba a ji martanin Hama Amadou ba, makusantansa sun ce ya yi tafiya zuwa birnin tarayya Abuja da ke Najeriya.

Alhaji Sidi Mairakumi, wani dan jam’iyyar Lumana ne, ya ce sun yi bakin ciki akan abinda ya faru amma zasu jira su ji abinda jogoran nasu zai ce akan lamarin.

A karshe kotun ta ce, za ta mika sunayen wadanda ke da iznin shiga zabe hannun ofishin Ministan cikin gida, wanda kuma ke da alhakin damka su ga hukumar zabe ta kasa.

Mukarraban babbar jam’iyyar ‘yan hamayya sun ce nan gaba kadan zasu bayyana matsayinsu a jam’iyyance game da wannan mataki da ke zuwa a wani lokacin da muhawara ke kara zafi a fagen siyasar Nijer, musamman a tsakanin magoya bayan Hama Amadou da na dan takarar jam’iyar PNDS mai mulki Bazoum Mohamed.

Ga Souley Moumouni Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Tsarin Mulkin Nijer Ta Cire Hama Ahmadou Daga Sunayen ‘Yan Takarar Shugaban kasa